Mutane 30 suka jikkata, kayan Miliyoyin Naira sun kone a Gobarar tankar Mai dake Legas

Mutane 30 suka jikkata, kayan Miliyoyin Naira sun kone a Gobarar tankar Mai dake Legas

Gobarar tankar Gasoline a Iju-Ishaga, Legas jiya, Alhamis ta jikkata mutane 30 da lalata motoci 15 kamar yanda Rahotanni suka bayyanar.

Da Misalin Karfe 3 na yamma ne lamarinnya faru yayin da ake sauke Gasdin da motar ta dauki. Wani guri ne dake diga daga jikin motar ya haddasa lamarin.

Gidaje 23 da shaguna 35 ne suka lalace inda gobarar ta bata kaya na Miliyoyin Naira. Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas, LASEMA, Nosa Okunbor yace babu mutum ko 1 da ya rasa ransa a hadarin.

\

Jami’an tsaro da sauran kungiyoyin Agaji sun halarci wajan.

Read Also:  An kai Hari Akan Tawagar Dan Takarar Gwamnan Ondo a PDP, Jegede yace Yunkurin Kashe shi akayi

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.