Shugaba Buhari ya aikawa jama’ar Kaduna sakon ta’aziyyar rasuwar Sarkin Zazzau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana kaɗuwarsa da alhinin rasuwar mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, kamar yadda wani saƙon ta’aziyya da mai taimaka wa shugaban kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar.

Saƙon ta’aziyyar, wanda shugaban ya aika wa Gwamna El-Rufa’i da kuma mutanen jihar Kaduna, Buhari ya ce Najeriya ta yi babban rashin ɗaya daga cikin sarakunan gargajiya da suka daɗe.

Ya kuma ce ba za a taɓa mantawa da gudunmuwar da Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya bayar wajen tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya tsakanin ƴan Najeriya ba a shekaru masu zuwa.

\

Shugaban ya kuma yi roƙon Allah ya gafarta wa marigayin, Ya kuma ba iyalansa da waɗanda suke ƙarƙashinsa juriyar babban rashin da suka yi.

Read Also:  Rikicin NBA: Lauyoyi sun huro wuta a cirewa Minista mukamin ‘SAN’

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here