Sarkin Zazzau ya rasu

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un

Allah ya yiwa me martaba sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris Rasuwa.

Rahoton da Hutudole ke samu shine Sarkin ya rasune a Asibitin sojoji na 44 dake garin Kaduna. Sarkin ya rasu yana da shekaru 84 a Duniya, ya kuma shafe shekaru 45 akan mulki.

\

Muna fatan Allah ya jikansa.

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi ne Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi da ne, dan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo.

\
Read Also:  Hotunan cikin katafaren gidan Rihanna na London wanda za a siyar a 14 biliyan

Shi kuma Sarki Muhamadu Sambo da ne, kuma na biyu a cikin ‘ya’yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a daular Fulani karkashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Danfodiyo ya yi a kasar Zazzau, kuma shi ne ya assasa gidan Katsinawa a sarautar Zazzau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here