Allah Yama Sarkin Zazzau Shehu Idris Rasuwa

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa.

Ya rasu ranar Lahadi.
Uban Garin Zazzau kuma Hakimin Soba, Alhaji Bashir Shehu Idris wanda ɗa ne ga marigayin shi ne ya tabbatar wa da BBC labarin.

Rahotanni solar ce Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya ta mako biyu a wani asibiti da ke Kaduna.

\

Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani.

Read Also:  Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un! Zariya Bata Taba Cika Irin Ta Yau Ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here