Ya kamata ka sani, ƴan Nigeria na shan bakar wahala – Jega ya aikawa Buhari sako

 

Ya kamata ka sani, ƴan Nigeria na shan bakar wahala - Jega ya aikawa Buhari sako

Attahiru Jega, tsohon shugaban INEC da John Onaiyekan, jigon Katolika solar koka kan halin da yan Najeriya ke ciki

Solar bukaci shugaba kasar Muhammadu Buhari ya dauki matakin da ya dace

\

Jega ya ce yan Najeriya na fama da wahala biyu na rashin tsaro da annobar korona

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega; da tsohon shugaban malaman Katolika a Abuja, Cardiac John Onaiyekan, solar yi martani kan halin da jama’a ke ciki.

\

Solar fada ma shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yan Najeriya na fuskantar wahala biyu na rashin tsaro da kuma na annobar coronavirus.

Don haka solar yi kira ga Shugaban kasar da ya yi duk abunda zai iya domin magance matsalar tsaro koda hakan na nufin sallamar shugabannin tsaro.

Solar bayyana hakan a cikin wani jawabi mai taken, ‘Ya shugaban kasa, Gwamnoni: Yanzu ne lokacin tattaunawa’ a ranar Lahadi.

Jawabin na dauke da sa hannun Jega, Onaiyekan, Janar Martin Agwai, Amb. Fatima Balla, Farfesa Jibrin Ibrahim, Misis Aisha Muhammed-Oyebode, Dr. Nguyan Feese.

Read Also:  KARFE !!! Sarkin Zazzau ya rasu

Sai Dr. Usman Bugaje da Dr. Chris Kwanja, dukkaninsu mambobin kungiyar Najeriya kan zaman lafiya da shugabanci nagari ne.

Jawabin ya zo kamar haka: “Najeriya, kamar dukkanin kasashen duniya tana fama da annobar korona. Sai dai, al’umman Najeriya na fuskantar wahala biyu ne saboda suna kuma fama da rashin tsaro da rikici a fadin kasar.

“Ya zama dole gwamnatin Najeriya ta dauki matakin gaggawa wajen magance hauhawan rashin tsaro, idan tana son cimma nasara a yaki da annobar. Wani binciken USIP na bayan nan a Najeriya ya gano sabon alaka tsakanin COVID-19, rashin zaman lafiya da kuma rikici.

“Musamman, binciken ya gano cewa wadanda rikice-rikice ya cika dasu ba za su aminta da matakan gwamnati na yaki da annobar korona ba idan aka kwatanta su da wadanda rikicin bai shafa ba.

Read Also:  An Naɗa Sabon Shugaban Kasa Na Riƙon Kwarya A Mali Bah Ndaw.

Solar kuma bayar da shawarwari kan yadda gwamnatin Najeriya za ta iya karfafa kokarinta na daidaita annobar ta hanyar magance rashin tsaro a fadin kasar.

“Garkuwa da mutane don kudin fansa ya kasance babban abun damuwa a fadin kasar. Yankin arewa maso gabas na fuskantar fawowar ayyukan Boko Haram, sannan yan bindiga solar mayar da dubban mutane marasa galihu a fadin garuruwan karkara a arewa maso yamma.

“Miyagun ayyuka a yankunan karkara na kara tabarbarar da lamarin tsaron abinci, domin manoma da dama basa iya zuwa gonakinsu tsawon watanni da dama saboda tsoron rasa ransu,” in ji kungiyar.

Solar yi kira ga Shugaban kasar a kan ya shirya wani tsari na tattaunawa domin magance rikici da ake samu na kabilanci da na addini.

Kungiyar ta ce majalisar kasa a jiha ya jagoranci shirin tattaunawar a matakin kasa yayinda kungiyar gwamnonin Najeriya za ta tabbatar da lamarin ya isa ga talakawa.

Solar bayyana cewa rikici tsakanin makiyaya da manoma ya yi sanadiyar rasa dubban rayuka a kasar sannan yana kara zurfafa rikicin kabilanci amma yan tsirarun mutane aka hukunta kan haka.

Read Also:  Sarkin Rano Autan Bawo Ya Mutu Amma Ana Zargin Mutuwar Tasa Da Wannan Dalili

Don haka kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta yi umurnin sake bincike a kan dukkanin rikicin makiyaya da manoma na baya.

Solar bukaci gwamnati da ta sallami shugabannin tsaro idab hakan ne zai kawo ci gaban abubuwa.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.