GL Trends


GIST | NEWS | COMEDY

MUSIC PROMO   ADVERTISE HERE   GIVEAWAY


« | »

Hausa Gist

Mai sayar da burkutu ta yi wa ƴar sanda duka saboda N150,000, ta yaga mata kaya

Posted by on September 14, 2020

Mai sayar da burkutu ta yi wa ƴar sanda duka saboda N150,000, ta yaga mata kaya

Wata mata mai suna Florence ta gurfana a gaban wata kotun majistare a kan zarginta da ake da dukan ‘yar sanda tare da yaga mata kaya

Florence Samuel tana da shagon burkutu wanda ‘yar sanda ta je kama wadanda ake zargin da satar N150,000

Ana zargin Florence da dukan ‘yar sanda, hada kai wurin aikata laifi, sata da hana zaman lafiya tare da tada tarzoma

\

Wata kotun majistare da ke zama a Osogbo da ke jihar Osun ta gurfanar da wata mata mai suna Florence Samuel a ranar Juma’a, sakamakon zarginta da ake da dukan ‘yar sanda mai mukamin sajan, Caroline Olaitan.

Florence mai shekaru 28 tana siyar da burkutu a wani shago da ke yankin Balogun Agoro a Osogbo. An zargeta da dukan ‘yar sandan tare da hana a kamata bayan Caroline da ziyarci shagonta.

\
Read Also:  Ambaliya a jihar Bauchi: Mutane 16 sun mutu, gidaje 2000 sun salwanta

Kudi har N150,000 mallakin wani mutum suka bace a shagon, lamarin da yasa ta zamo abin zargi.

An gurfanar da mai siyar da burkutun a kan laifukan da suka hada da cin zarafi, hana zaman lafiya, hada kai wurin aikata laifi da sata.

Lamarin ya faru a ranar 10 ga watan Satumban 2020, wurin karfe 9:45 na protected yayin da wani kwastoma mai suna Taiwo Yusuf ya ziyarci shagonta amma kudinsa N150,000 ya bace.

An gurfanar da ita tare da wani Ogundipe mai shekaru 59, wanda ake zarginsu da hada kai da shi wurin aikata laifin.

Dan sanda mai gabatar da kara, Adeoye Kayode, ya yi bayanin cewa Florence ta yi wa Caroline mugun duka tare da yaga mata kaya a yayin da taje kama ta.

Read Also:  An Kashe Fasinjoji 10 Tare Sace Wasu Da Yawa A Wani Hari A Borno

Wannan laifin ya ci karo da sashi na 356, 249, 251, 516 da 390 na dokokin laifukan jihar Osun na 2002.

Wadanda ake zargin solar musanta aikata laifin.

Lauyan masu kare kansu, Najite Okobe, ya bukaci kotun da ta bada belin wadanda yake karewa.

Amma kuma, Adeoye ya soki bukatar belin inda yace hakan zai iya shiga tare da hana samun duk wata shaida da ta dace.

Alkalin kotun, Adebayo Ajala, ya bada belin wadanda ake zargin a kan kudi N400,000 kowannensu tare da tsayyaye guda daya.

Ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Oktoban 2020.

A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Ladidi Abbas, a ranar Talata ta maka mijinta mai suna Shehu Abbas a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke zama a Magajin Gari, a Kaduna.

Read Also:  Hotuna: Fusatattu sun kashe tare da kona wasu barayi da aka kama a Calabar

Ladidi ta bukaci mijinta da ya sauwake mata igiyoyin aurensa, saboda dukan da take sha a hannunsa a duk lokacin da suka samu matsala, jaridar The Nation ta wallafa.

Post Views: 674


CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Share this post with your Friends on

 

No Comments Yet

Leave a Reply


Go Back To The Top


« | »


Looking for a song? Search below


MUSIC

VIDEO